Shafin Farko Sashin Blog Hanyar Tuntuba

Tauraron Zamani » Blog » Yadda ake bude E-mail da Google wato Gmail

Yadda ake bude E-mail da Google wato Gmail

Wallafan July 3, 2019. 10:36pm. Na Tauraro Adon Samaniya. A Sashin Abubuwa Goma

YADDA AKE BUDE GMAIL ACCOUNT
Gmail account dinka, shi ne Google account,
kuma idan ka mallaki Gmail Account, zaka iya
amfani da username da password din daka bude
kayi amfani dashi wajen bude wurare kamar
haka;
+ YouTube,
+ Google+,
+ GTalk
+Google Play, da kuma
+ Google Drive.
Wadannan sune sauran google Product, wadanda
basa sarrafuwa sai da gmail account.
Idan nace Gmail Account wasu sukan dauka, shi
Gmail, yana matsayinsa na Gmail saboda da haka
Yahoo shi ne email. Ba haka bane, dukkansu
kowannensu mail ne, hasalima Gmail yafi yahoo
muhimmanci, saboda akwai abubuwan da basa
sarrafuwa yadda ya kamata matukar babu shi,
kamar wadanda na lissafo asama, amma shi
Yahoo bashi da irin wadannan wuraren dayawa,
imma akwai.
Sannan zaka iya bude Gmail ta cikin ko wanne
daya na wadancan account dana. Lissafa, kuma
yayi aiki adukkansu, sannan shi Gmail account
zaka bude shi ne, sannan ka samu Google+ kai
tsaye, saboda suna tare da Gmail a hade, zasuyi
amfani da profile dinka ne, su kirkirar maka
Google+.
Misali idan ka bude gmail ta Youtube, ko kuma
ka shiga Youtube kasa Gmail dinka, zaka samu
damar dora Video akan shafin, baima tsaya nan
ba, zaka samu damar yadaa Document dinka a
Google Documents.
Da farko idan kana bukatar bude Gmail Account,
saikaziyarci shafin gmail.com zaka inda kasa
"Create Google Account" saika latsa wurin.
Ka zabi sunan kasarka, sannan Kasa Lambar
wayarka idan sun bukaci hakan, kuma kasa
lamba wacce ka tabbatar tana aiki, kuma. Tana
kusa da kai, domin idan kasa lambar wayarka
zasu turo maka da Link wanda zaka bi domin ka
Mallaki Gmail dinka kai tsaye.
Amma ka tabbata kasa Username dinka wanda
ya dace kuma bazaka manta ba, sannan kasa
password dinka wanda kasan bazaka. Manta da
shiba, username dinka shine kamar. Haka;
username@gmail.com
tauraro@gmail.com
facebook@gmail.com
gwankia6@gmail.com
Wadannan duka musalai ne nake baka, saika
tsara naka. Yadda ya dace, sannan ana iya sa
masa lamba agabako a farko, ko a tsakiya,
misali:
tauraro2019@gmail.com
tauraro01@gmail.com
face23book@gmail.com
Amma shi wannan yana faruwane a dayan biyu.
1. Zaka iya amfani da lamba idan kasa naka
amma akwai wani mai irinsa, dole bazasu karba
ba, saika bam-banta.
2. Ko kuma kana da ra'ayin saka lambar.
Kasanipassword na gmail naka, dole ya zama
daga harafi 8 zuwa 32, sannan. Basa karbar
Dictionary words.
Kana iya bude. Gmail akowanne wuri, sannan
kuma tayi maka amfani aduk inda ya dace.

Tura wannan zuwa:

Game da Mawallafi:

Babu hoto
Tauraro Adon Samaniya

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Yadda ake bude E-mail da Google wato Gmail"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Sanarwa!

wannan shafi ana kan aikin sa ne a halin yanzu...

Kasidu Masu Alaka

  • Hoton kasida mu sha dariya
    "LABARIN MU KYAKYATA" Wasu mutane ne suka yi hatsari a hanya sai governor yazo wucewa ta hanyar ya gani sai yace a irga matattu da kuma wadanda suka ...Budo cikakke
  • Hoton kasida Ramuwa ko mugunta
    musha dariya acikin wannan labari na: Wani Bakatsine da wani Banupe ne su ka yi laifi, sai a ka kai su kotu. Ga yadda zaman kotun ya kasance. *Alkali:...Budo cikakke
  • [Hoton kasida] Alhaji Aliyu Mai Bornu
    A jikin takardar kudi ta naira Dubu daya akanga hotunan mutane biyu, daga cikinsu akwai maisuna Alhaji Aliyi Mai bornu. Saidai da yawa wasu basusan wa...Budo cikakke