Shafin Farko Sashin Blog Hanyar Tuntuba

Tauraron Zamani » Blog » Mairo Mai tonan silili

Mairo Mai tonan silili

Wallafan April 20, 2019. 12:28am. Na Tauraro Adon Samaniya. A Sashin Mudara
HAJIYA MERO MAI TONON SILILI..! Awata kotu ne ana sauraron kara, jama'a sun cika makil, sai alkali ya bukaci wata tsohua ta fito donin bayar da shaidar wanda ya kawo kara an sace masa mota. Da tsohuwa ta fito, sai lauyan wanda yakawo kara ya fito domin yima tsohuwa tambayoyi kamar haka: Lauya: Baaba shin ko zaki iya gayawa kotu sunanki? Tsohuwa tace, "Ni sunana HAJIYA MERO MAI TONON SILILI. Lauya ya sake tambayarta ko HAJIYA MERO MAI SILILI kinsan ni waye? Tsohuwa ta gyara tsayuwarta, sannan tace " Eh mana nasan ka aitun kana karaminka, kai makaryaci ne, ka'iya hada waje, gaka da yaudara da kuma rashin iya magana, ga gulma da kuma shaye shaye da neman mata. Lauya jikinsa yayi sanyi cikin alamun jin kunya yaje kusa da abokin aikinsa, wato dayan lauya sai ya cewa tsohuwar "Baaba wannan fa ko kinsan shi? Tsohuwa ta gyara mayafin dake rataye akafadunta tace, Toh ai gyara kaima akan wannan domin, wannan kam ai asalin cikakken dakiki ne gashi da shegen son jin gulma ga kuma muna furci, kai bari kaji yanzu haka yana cin amanar matarsa da wasu matan banza guda uku kuma daya daga cikinsu ma matarka ce Lantana". Tana rufe baki sai alkalin kotun wanda tunda aka fara shari'ar baice komai ba, yana sauraron wannan tsohuwar yadda take fede biri har wutsiya. Sai alkali ya kira dukkanin lauyoyin cikin murya kasa_kasa yace, "kunsan Allah duk shegen daya kuskura ya tambayi wannan tsohuwar ko ta sanni tabbas zaici ubansa kuma sai nasa an kwace masa lasisinsa na aiki... Hehehehehehe!!! Ni kuma duk wanda ya tambaye ta ko ta sanni sai na sa ya sake karanta wannan (kasida). Hahahahahahahahahahahaha!

Tura wannan zuwa:

Game da Mawallafi:

Babu hoto
Tauraro Adon Samaniya

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Mairo Mai tonan silili"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Sanarwa!

wannan shafi ana kan aikin sa ne a halin yanzu...

Kasidu Masu Alaka

  • Hoton kasida Barka da Zuwa
    Barka da ziyara! wannan shafin ya kasance sabo ne. A wannan sashen ne zaka koyi komi da komi dangane da yanar gizo. ...adakace mu
  • Hoton kasida Ramuwa ko mugunta
    musha dariya acikin wannan labari na: Wani Bakatsine da wani Banupe ne su ka yi laifi, sai a ka kai su kotu. Ga yadda zaman kotun ya kasance. *Alkali:...Budo cikakke
  • [Hoton kasida] Menene Tauraron Dan'adam
    Tauraron dan Adam, kamar yadda bayani ya gabata, shine duk wata na'ura mai cin gashin kanta da ake harbawa zuwa sararin samaniya don mikawa da karbo...Budo cikakke