Shafin Farko Sashin Blog Hanyar Tuntuba

Tauraron Zamani » Blog » Tarihin Marigayi justice Mamman Nasir katsina.

Tarihin Marigayi justice Mamman Nasir katsina.

Wallafan April 26, 2019. 5:15pm. Na Abubakar A Gwanki. A Sashin Magabatan mu
Takaitacen tarihin Marigayi Justice Mamman Nasir: An haifi Jastis Nasir a shekarar 1929 a jihar Katsina. Ya yi karatun makarantar sakandire a Kaduna, inda ya samu takardar shaidar kammala karatun sakandire ta kasashen yammacin Afrika (WAEC) a shekarar 1947. Marigayin ya halarci jami'ar Ibadan kafin daga bisani ya wuce kasar Ingila, inda ya kammala karatunsa na digiri a bangaren shari'a a shekarar 1956. Bayan dawowarsa Najeriya a shekarar 1956, an nada shi a matsayin alkali kafin daga bisani a nada shi a matsayin minista shari'a, na yankin arewacin Najeriya, a shekarar 1961, mukamin da ya rike na tsawon shekaru biyar. Marigayi Justice Mamman Nasir ya nemi goyon bayan 'yan PDP A shekarar 1967 ne aka nada shi a matsayin darektan sashen gurfanarwa na yankin arewa kafin daga bisani ya zama mai kula da shari'a a yankin arewa ta tsakiya, mukamin da ya rike har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin daya daga cikin alkalan kotun koli a shekarar 1975. A shekarar 1978 ne aka nada shi a matsayin shugaban kotunan daukaka kara na Najeriya, mukamin da ya rike har zuwa lokacin da ya yi ritaya a shekarar 1992,shekarar da aka nada shi a matsayin Galadiman masarautar Katsina. Ya kuma rasu ranar Asabar 13 ga watan Afrilun 2019. Allah ya jikan MAZAN JIYA(MAGABATANMU). DAGA: BASHIR A SANI D/JARI GWANKI

Tura wannan zuwa:

Game da Mawallafi:

tmp-cam--90533954.jpg
Abubakar A Gwanki
Abubakar A Gwanki, dalibi mai neman ilimi

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Tarihin Marigayi justice Mamman Nasir katsina."

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Sanarwa!

wannan shafi ana kan aikin sa ne a halin yanzu...

Kasidu Masu Alaka