Shafin Farko Sashin Blog Hanyar Tuntuba

Tauraron Zamani » Blog » Mu kyakyata

Mu kyakyata

Wallafan April 19, 2019. 3:09pm. Na Tauraro Adon Samaniya. A Sashin Abubuwa Goma
Mu Kyakyata Na wani saurayi da budurwa adakin karatu: Wata kyakykyawar yarinya ce budurwa ta shiga Library watau dakin-karatu ta sami wuri ta zauna tana karatu saiwani Hadadden saurayi matashi shima ya shigo sai ya nufi inda take zaune yace mata, "don Allah ko zan iya zama a wannan kujerar dake kusa dake? Don na duba ko'ina ba wurin zama sai nan kadai" Sai yarinyar nan ta daga murya da karfi yadda kowa zai ji a wurin tace "don Allah Malam ka tafi ka bani wuri ni ba 'yar iska bace da kake cewa zaka bani naira dari biyar don in bika dakinka ka zubar mun da mutuncina" sai duk mutanen dake wurinnan makil kowa ya waigo cikin mamaki yana kallon saurayin nan, shi kuwa saurayin nan ya rasa abin fadi sai dai ya dukar da kai kasa duk kunya ta isheshi saboda yadda yarinyar nan ta tsinkashi ta zubar masa da mutunchinsa ba gaira ba dalili bai mata komai ba. Amma duk da haka sai yayi karfin hali yaje gefen window ya tsaya ya bude littafinsa ya soma karatunsa don jarabarwar da zasu yi. Sai yarinyar nan taga bata kyautaba abinda tai masa sa ta taso tazo wajen yaron nan dake tsaye ta kwantar da muryarta kasa tayi masa rada tace, "Don Allah malam kayi hakuri fa na tsinka ka a cikin mutane abin da yisa nayi maka haka shine don karatun da nake na fannin halayyan mutane ne kuma akansa nake nazari don za muyi jarabawa akan darasin fushin namiji, shi yisa nayi abin da zai baka haushi don in rubuta" Sai saurayin nan data kunyata ya kalli yarinyar nan cikin mamaki sannan ya daga muryarsa da karfi yadda kowa a wurin zai ji yace"tabdi ai ba ki kai kyawun da har za ki biyoni nan kice sai na ba ki naira dubu biyar ba sannan za ki yarda in kwana dake ba, me kike dashi har na naira dubu biyar? Ki kare kawai ki sa mun ciwon kanjamau a banza! Don Allah tafi ki bani wuri na fasa banso" sai yarinyar nan ta fadi kasa sumammiya don tsananin kunyar irin tsinkawar da saurayin nan yayi mata akan ramuwar abin da tayi masa. Hahahahahahahahahahahahaha!! Me xaku ce??http://zamaniweb.com/administrator/files/19/04/168/mukyakyta.jpg

Tura wannan zuwa:

Game da Mawallafi:

Babu hoto
Tauraro Adon Samaniya

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Mu kyakyata"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Sanarwa!

wannan shafi ana kan aikin sa ne a halin yanzu...

Kasidu Masu Alaka

  • Hoton kasida mu sha dariya
    "LABARIN MU KYAKYATA" Wasu mutane ne suka yi hatsari a hanya sai governor yazo wucewa ta hanyar ya gani sai yace a irga matattu da kuma wadanda suka ...Budo cikakke
  • [Hoton kasida] Menene Tauraron Dan'adam
    Tauraron dan Adam, kamar yadda bayani ya gabata, shine duk wata na'ura mai cin gashin kanta da ake harbawa zuwa sararin samaniya don mikawa da karbo...Budo cikakke
  • [Hoton kasida] Danfulani a Makka
    'dan fulani yaje aikin hajji a makkah sunyi kwana (6) a saudiya da ranan juma a' tazo sai dan fulani ya shiga cikin masallaci saboda yin sallan jum...Budo cikakke