
A yan kwanakinnan ne dai ake ta yada hotinan wadannan yara a shafukan sada zumunta Kowa na tofa albarkacin bakinsa a game da auren da akayimasu ma wuri duba da karancin shekarun su.
To kome hukimar kare hakkin yara tace dangane da auren wuri?
AUREN WURI HARAMUNNE!
Wata gidauniyar tallafa wa kananan yara ta fada a cikin wani sabon rahoto cewa 'yan mata kimanin miliyan bakwai da rabi ake yi wa aure ba bisa ka'ida ba duk shekara.
A cewarta ana aurar da 'yan mata, suna kasa da shekaru mafi karanci da dokokin kasashensu suka kayyade.
Kungiyar Save the Children ta ce ana yin kashi 1 cikin 4 na duk auren da ta ce haramtattu ne a yankin yammaci da kuma Afirka ta tsakiya, inda ake tilasta wa yarinya 'yar shekara 12 yin aure a Senegal da kuma 'yar shekara 15 a Saliyo.
Sau da yawa yaran kan fito ne daga gidan da daya daga cikin mahaifa ya mutu, kuma suna da yiwuwar samun juna biyu da kuma aske makaranta.
Kungiyar ta bukaci illahirin kasashe su sanya shekara 18 ta zama mafi karancin shekarar aure ga 'ya mace.