Shafin Farko Sashin Blog Hanyar Tuntuba

Tauraron Zamani » Blog » Almajiranci

Almajiranci

Wallafan May 11, 2020. 12:13pm. Na Abubakar A Gwanki. A Sashin Al adun Hausa
http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/almajiri.jpg

Almajiranci tsarine na koyon ilimin Alkur'ani a tsangayu. Akasari anfi yin wannan tsarine a Arewacin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar. Amma kuma anayin wannan tsarin a wasu kasashen da dama a Yammacin Afrika.

Tsarin Almajiranci tsarine wanda iyaye ke tura yaransu kanana tun daga kimanin shekara bakwai da haihuwar su wani lokacin ma har kasa da haka, su bi malamai zuwa nesa da garuruwan su domin yin karatun Alkur'ani. Akasari Almajirai kan yi karatunsu tsakanin shekar 3 zuwa 12 da haihuwa. Wasu Almajiran kan koma garuruwansu ganin mahaifansu bayan shekaru da turasu. Saidai kuma wasu Almajiran kan koma ga iyayen su ne da zarar sun samu sauka, wasu kuma koda sun sauka suna cigaba da zama a tsangayu domin zurfafa ilimin su na Alkur'ani da ma na Fikihu.
Bayan Almajirai sun kammala karatunsu wadanda suke a karkara kan koma kauyikansu domin yin aiyukan gona. Wandan da suke a birane kuwa kan fara yin kananun sana'u kamar shushana, saida shayi da sauran su.

ASALIN KALMAR ALMAJIRI

Ita dai kalmar Almajiri ta dauko asali ne daga harshen Larabci wato " ﺍﻟﻤُﻬَﺎﺟِﺮْ " "al-Muhajirun," wanda ke nufin "wanda yayi kaura daga gidansa zuwa wani nesan waje domin neman ilimin addinin musulunci" hakanan a Hausance kalmar akan fadadata ne zuwa ga dukkan wani mabaraci wanda yake bara mace ko namiji koda kuwa baya neman ilimin addini.
Mutane na bayar da sadaka ga almajirai domin taimaka masu tare da neman lada a gurin Allah. Sannan kuma sukan basu sadaka domin karfafa masu gwiwa akan neman ilimin addinin musilunci.

AKASARIN ALMAJIRAI

Yawa yawan almajirai yayayen talakawa ne wadanda suke barin iyayen su domin bin malamai zuwa tsangayu domin neman ilimin Alkur'ani.

MARTANIN MUTANE

Daga cikin martanonin da mutane ke mayarwa kan Almajiranci da Almajirai sun kasu zuwa kaso biyu.
Kaso na farko na kallon Almajiranci shine kadai ko hanyace sahihiya ta samun ilimin addinin Musulunci tare da tarbiyar da yara da samar da al'uma ta gari.
Dayan bangaren kuma akasarin haka ne. Suna kallon Almajiranci a matsayin tauye hakkin yara (musamman kungiyoyin kare hakkin dan adam da kare hakkin yara). Haka kuma dayawa jama'a wasu na kallon Almajiranci da samar da yan ta'addan musamman ma n Boko Haram wadanda suke ganin haramun ne ma ilimin boko.

Tura wannan zuwa:

Game da Mawallafi:

tmp-cam--90533954.jpg
Abubakar A Gwanki
Abubakar A Gwanki, dalibi mai neman ilimi

An yi sharhi 3 a kan "Almajiranci"

2020-06-23 03:19:59

Cialis Viagra En Ligne https://agenericcialise.com/ - Cialis Zithromax Doses cialis generic release date Amoxicillin Synthesis

2020-08-20 00:03:07

levitra contraindications Esosaulp https://artsocialist.com/ - buy cialis online forum amoupE does caffen effect cialis Boomohoops Cialis rogupseree Medications Like Seroquel

2020-09-14 13:33:32

Effectiveness Of Keflex For Uti Esosaulp https://biracialism.com/ - Cialis amoupE Xopenex Boomohoops canadian pharmacy cialis rogupseree Cialis Temoignage

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Sanarwa!

wannan shafi ana kan aikin sa ne a halin yanzu...

Kasidu Masu Alaka

  • [Hoto] Mu kyakyata
    Mu Kyakyata Na wani saurayi da budurwa adakin karatu: Wata kyakykyawar yarinya ce budurwa ta shiga Library watau dakin-karatu ta sami wuri ta zauna ta...Budo cikakke
  • [Hoto] Tarihin Mallam Ja'afar Mahmud Adam Kano
    Ja'afar Mahmud Adam Ya rayu ne daga watan Fabrairu 12 na shekara ta 1960 zuwa 13 ga watan Afrilun shekara ta 2007. Yarasu ne sanadiyar harbin sa da ...Budo cikakke
  • Hoto Ni shadi
    Labarin wani saurayi da budurwarsa: Wani saurayine yaje zance wajen budurwarsa , suna tsakiyar hira sai aka fara ruwa kamar da bakin kwarya har zuwa d...Budo cikakke