Shafin Farko Sashin Blog Hanyar Tuntuba

Tauraron Zamani » Blog » Alhaji Aliyu Mai Bornu

Alhaji Aliyu Mai Bornu

Wallafan April 21, 2019. 1:41pm. Na Abubakar A Gwanki. A Sashin Magabatan mu
A jikin takardar kudi ta naira Dubu daya akanga hotunan mutane biyu, daga cikinsu akwai maisuna Alhaji Aliyi Mai bornu. Saidai da yawa wasu basusan wanene Alhaji Aliyu Mai bornu ba.

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/04/168/aliyu_mai_bornuAliyu Mai bornu.

An haifi Mai Bornu a garin Yola, acikin iyalan kabilar kanuri. Mai Bornu yayi karatu a makarantar Elementare a Yola, sai Makarantar Yola Middle School, sai ya Samu shiga makarantar Kaduna College a 1939, ya kammala a 1942 a matsayin malami mai koyar da harshen Turanci. Ya fara koyarwa a inda yayi karatu wato makarantar Yola Middle School daga 1942-1946, sai kumadai ya tsinci kansa a dayar makarantar da yayi karatu cikinta wato Kaduna College takanin 1946-1952, a nanne ya shiga kungiyar malaman makarantar ta arewa wato (Northern Teachers Association). A1952, ya dawo Yola a matsayin mataimakin hedimasta na makarantar Yola Middle school. Mai Bornu ya samu tallafin karatu na gwamnati zuwa kasar Birtaniya inda ya karanta Tsumi da Tattai (Economics) a makarantar Bristol University inda ya kammala a 1957.
Bayan dawowar sa gida Najeriya ne kuma Mai Bornu ya kama ayyuka a fannin bankuna inda ya rike shugaban babban bankin Najeriya (Central Bank of Nigeria CBN), kuma shine dan Najeriya na farko da ya fara rike wannan matsayin.

Tura wannan zuwa:

Game da Mawallafi:

tmp-cam--90533954.jpg
Abubakar A Gwanki
Abubakar A Gwanki, dalibi mai neman ilimi

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Alhaji Aliyu Mai Bornu"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Sanarwa!

wannan shafi ana kan aikin sa ne a halin yanzu...

Kasidu Masu Alaka